A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal Muslimin Ibrahim Anjum Shujaa, a wata tattaunawa, ya yi nuni da tarihin yakin labarai, yana cewa: "wannan lamari ba sabon abu ba ne, tun daga farkon Musulunci akwai misalai karara a kansa, ciki har da abubuwan da suka faru a Siffin, Uhud da Badr; inda ƙirƙirar labari da tasiri kan ra’ayoyin jama’a suka taka rawa wajen fayyace makomar yake-yake."
Ya kara da cewa: "A wannan zamani ma maƙiyi yana mai da hankali kan tunanin mutane da fahimtarsu, yana kokarin gurgunta al’umma daga ciki ta hanyar cusa tunanin rashin ƙwarewa, raunana kwarin gwiwa da haifar da yanke kauna; saboda haka ne ake jaddada batun Jihadut-Tabyeen a matsayin amsa da ta dace da sabon yanayin fagen yaƙi."
Wannan mai binciken harkokin addini ya yi nuni da maganganun Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, yana mai cewa: "Idan ba a bayyanawa hakikanin al’umma, nasarorin juyin juya hali, tsaron kasa mai tsarki da gaskiyar tarihi yadda ya kamata ba, maƙiyi zai karkatar da su ya nuna su a bisa akasin gaskiya; har ya kai ga sauya matsayin azzalumi da wanda aka zalunta, har ma da shahidi da makashi."
Ya ci gaba da cewa yakin labarai shi ne muhimmin salon maƙiyi a yaƙin fahimta, yana cewa: "Kayan aikin wannan yaƙi shi ne kafafen watsa labarai, amma abin da ya fi muhimmanci a nan shi ne “masu kafafen watsa labarai” da kuma masu fafutuka da ke samar da labarai, yadawa da kuma tabbatar da su."
Hujjatul Islam Anjum Shujaa ya lissafo ka’idoji shida na Alkur’ani domin samun rinjaye a yaƙin labarai, yana cewa: "Bayyanawa da tantance labari, kauce wa yaɗa labarai cikin gaggawa, komawa ga masana da ma’abota ilmi, kyakkyawan zato, muhawara ta gari da kuma basira, su ne ka’idojin da za su iya kare al’umma daga karkatarwa, jita-jita da yakin fahimta."
Game da hanyoyin dawo da bege (fata) cikin al’umma kuwa, ya bayyana cewa: "Domin tinkarar kokarin maƙiyi na haifar da yanke kauna, dole ne a farfado da sarkar “yin wasiyya da gaskiya da hakuri”, kuma maimakon taƙaita kai ga salon kariya kawai, sai a koma ga “jihadut-tabyeen na kai hari”; ma’ana, masu imani da masu juyin juya hali su kasance kullum taku daya a gaban maƙiyi."
Wannan malamin Hauza ya kuma yi nuni da rawar jama’a wajen kare juyin juya hali da goyon bayan jagoranci, yana cewa: "Ɗorewar wannan halartar jama’a tana rataye ne da manyan ginshikai guda biyu; na farko gaskiya da bayyana gaskiya daga masu alhaki ga jama’a, na biyu kuma haifar da bege ta hanyar bayyana nasarori da haskaka alkawuran Ubangiji da taimakonsa."
A ƙarshe ya jaddada cewa: "Idan al’ummar muminai suka tsaya kan manhajar Alkur’ani wajen mu’amala da labari da ruwaya, ba kawai za su tsira daga karkatarwa da juya gaskiya ba, har ma za a kiyaye da karfafa jarin zamantakewa, begen jama’a da kuma juriyar al’umma a tafarkin Juyin Juya Halin Musulunci."
Ra'ayinka